Isa ga babban shafi
Faransa

Paris: An dade ana sa ido kan direban da ya kai hari

Masu bincike a Faransa, sun ce direban motar da ya afka wa ‘yan sanda a Champs-Elysees da ke birnin Paris a tsakiyar ranar jiya Litinin, na daga cikin mutanen da jami’an tsaro ke sa wa ido tun shekara ta 2015, bisa zargin cewa yana hulda da masu tsatsauran ra’ayin addini.

Jami'sn kashe gobara sun samu nasarar zakulo gawar direban da ya afkawa motar 'yan sanda a Paris.
Jami'sn kashe gobara sun samu nasarar zakulo gawar direban da ya afkawa motar 'yan sanda a Paris. Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Tuni dai direban mai shekaru 31 a duniya ya mutu bayan kai harin, kuma daga bisani an gano bindiga, da tukunyar gas a cikin motarsa.

Gerrard Collomb, ministan cikin gidan kasar ya ce harin na jiya, wata alama ce da ke kara tabbatar da cewa kasar na cikin yanayi na barazana.

Dan haka, lamari ne da ke kara tabbatar da cewa barazanar ta’addanci ta karu a Faransa, kuma a cewar Collomb, a gobe Laraba zai gabatar wa taron majalisar ministocin kasar, daftarin doka da ke neman a tsawaita wa’adin aiki da dokar ta baci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.