Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa zata rufe tashoshin samar da makamashin nukiliya

Sabon ministan Muhallin kasar Faransa, Nicolas Hulot, ya ce gwamnati zata rufe akalla kashi daya bisa uku, na tashohin samar da lantarki daga makamashin nukiliya.

Ministan Muhallin kasar Faransa, Nicolas Hulot.
Ministan Muhallin kasar Faransa, Nicolas Hulot. REUTERS/Michel Euler
Talla

Hulot, ya ce, matakin na daga cikin manufofin gwamnatin Macron, na rage yawan hasken lantarkin da tashoshin makamshin nukiliyar ke samarwa.

A shekara ta 2015, tsohuwar majalisar faransa mai rinjayen `yan jam`iyyar socialist ta kafa dokar tilastawa gwamnatin kasar rage yawan lantarkin da tashoshin nukiliya ke samarwa daga kashi 75 a halin yanzu zuwa kashe hamsin kafin shekara ta 2025.

A lokacin da yake gabatar da sabon tsarin gwamnatin Macron kan muhalli, ga zauren majalisar kasar, Hulot ya ce za`a rufe tashoshin nukilya 17 daga cikin 58 da faransar ta mallaka, wanda take samun kudaden shiga euro biliyan 3 a duk shekara daga lantarkin da take saidawa makwabtan kasashe.

Mafi yawancin tashohin makamshin nukilyar Faransa dai zasu kammala aikinsu ne a shekar ta 2027, kasancewar an gina su ne a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980.

A baya dai kasan na dogaro da tashoshin kan samar da lantarki, to amma tunani ya sauya daga baya, sakamakon mummunan hadarin da ya auku a tasahar makamshin nukilya ta Fukushima da ke Japan a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.