Isa ga babban shafi
Turai

EU zata kira taron gaggawa kan gurbataccen kwai

Kwamishinan Lafiyar kungiyar kasashen Turai, EU, Vytenis Andriukaitis ya bayyana cewar kungiyar zata kira wani taron gaggawa kan matsalar gurbataccen kwan da ya mamaye nahiyar domin kawo karshen zargin junan da ake yi yanzu haka.

EU zata gudanar da taro kan gurbataccen kwai mai dauke da sanadarin Fipronil da ke yaduwa a Turai
EU zata gudanar da taro kan gurbataccen kwai mai dauke da sanadarin Fipronil da ke yaduwa a Turai REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Kwamishinan ya bukaci kasashen Netherlands da Belguim da Jamus da su daina zargin juna ko kuma cacar baki kan matsalar domin matakin ba zai shawo kan matsalar ba.

Jami’in ya ce abinda suka sa a gaba yanzu shine tattara bayanai da yin nazari a kan su domin daukar matakan da suka dace.

Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da irin wannan gurbataccen kwai a kasashe 11 na Turai, kuma ana fargabar ana iya samun su a wasu kasashen duniya.

Hukumar Kula da ingancin abinci a kasar Denmark ta ce an sayar da ton 20 na gurbataccen kwan da aka dauko daga Netherlands.

Hukumar ta ce kamfanin da ke sayar da amfanin gonar, ya karbi ton 20 daga masu ba shi kaya daga kasashen waje, kuma tuni aka sayar da wani sashe ga jama’a musamman gidajen abinci da kamfanoni.

Hukumar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike, kuma babu mamaki a samu wasu da ke da irin wannan matsala.

Kasashen da suka karbi irin wadannan gurbataccen kwan sun hada da Belguim da Jamus da Sweden da Switzerland da Birtaniya da kuma Faransa wacce ke cewa an siyar da gurbataccen kwan har dubu 250 a kasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.