Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na fuskantar koma baya fiye da Hollande

Sakamakon wata sabuwar kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Faransa ta nuna cewa yawan ‘yan kasar da suke nuna rashin gamsuwa da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ya karu daga watan Yuli zuwa yau.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Stoyan Nenov
Talla

Kuri’ar wadda jaridar Le Journal Du Dimanche da ake wallafawa a kasar ta jagoranta, ta nuna cewa kashi 57 da bakwai na ‘yan kasar sun dawo daga rakiyar gwamnatin Macron yayinda kashi 40 ne kawai suka bayyana gamsuwa da salon jagorancin gwamnatinsa.

Sakamakon kuri’ar dai ya nuna cewa raguwar farin jinin Macron ya fara fuskanta tun daga watan Mayu zuwa yanzu, ya zarta koma bayan da tsohon shugaban kasar ta Faransa Francois Holland ya fuskanta yayinda shima ke shirin cika kwanaki dari da kama aiki.

Tun bayan hawansa mulki Macron ya fuskanci koma baya kan manufar gwamnatinsa kan yi wa tsarin ayyukan kwadago garambawul, takkadama da rundunar sojin kasar, da ta kai ga cewa daya daga cikin manyan Hafsoshin sojin ya ajiye mukaminsa, da kuma matakin zaftare kudaden bada tallafin samar da gidaje da gwamnatinsa ta dauka, matakin da bai yiwa Faransawa da dama dadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.