Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan sandan Faransa sun fara kwashe Bakin-Haure daga Grande-Synthe

Jami’an tsaron Faransa aun fara aikin kakabe Bakin-Haure da suka yi sansani a dajin Grande-Synthe, dake arewacin kasar dab da kan iyakar gabar ruwan kasar da Ingila.

Wasu bakin-haure a sansanin Calais da ke arewacin Faransa yayinda suke dakon a raba musu kayan sawa.
Wasu bakin-haure a sansanin Calais da ke arewacin Faransa yayinda suke dakon a raba musu kayan sawa. RFI
Talla

A cewar hukumar dake kula da tafiye-tafiye da sa ido kan tsugunar da baki ta Faransa, sama da mutsugunai 400 ne aka kawar a wannan sansani domin sake tsugunar da su a wani sabon muhalli dake da tabbas.

A cewar magajin garin Mr Damien Carême, tsakanain bakin haure 350 zuwa 400 ne da ke zaune a sansanin dajin na Grande-Synthe, aka kwashe, sakamakon ci gaba da gurbacewar da yanayi ke yi, inda ya ce kidayar karshe da ma’aikatarsa ta gudanar, ta nuna cewa yara kanana 56 ne ke cikin tawagar bakin hauren,,dake rayuwa a dajin, yayinda mata suka zarta 40.

A farkon shekarar 2016 ne magajin Garin tare da hadin gyuiwar kungiyar bayar da agaji Médecins sans Frontières, ya buda sansanin na Grande-Synthe, ga bakin hauren, sansanin da ya mutunta duk wasu ka’idoji da kasashen duniya suka shata wajen ganin sansanin ‘yan gudun hijira ya tanada inda aka tsugunar da daruruwan Bakin-Haure, sai dai a cikin watan Afrilu sansanin ya hadu da mummunar gobarar da ta lalatashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.