Isa ga babban shafi
Amurka

Korea ta arewa za ta fuskanci Ladabtarwa - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa hanya daya ce ta rage ayi amfani da ita wajen Ladabtar da Korea ta arewa, bayan tsawon shekaru 25 da aka dauka ana neman tattaunawa da ita kan makamin Nukiliya ba tare da samun nasara ba.

A cewar Donald Trump shekaru 25 da aka shafe ana bin kan Korea ta arewa dangane da hada makamai masu linzami ya kawo karshe, yanzu dole ne a dauki matakin karshe a kanta.
A cewar Donald Trump shekaru 25 da aka shafe ana bin kan Korea ta arewa dangane da hada makamai masu linzami ya kawo karshe, yanzu dole ne a dauki matakin karshe a kanta. Reuters
Talla

A wani sako da Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Amurka ta shafe shekaru 25 ta na neman tattaunawa da Koriya ta arewa don kawo karshen hada makamai masu linzamin da ta ke yi,  amma har yanzu ba a samu nasara ba, yana mai cewa yanzu akwai hanya daya da za a yi maganin kasar.

A baya-bayan nan ne dai Kim Jung Un ya sanar da cewa kasar ta yi nasarar hada wani makami mai linzami da zai yi nisan zangon da bata taba hada kamarsa ba.

Trump dai ya yi gargadin cewa, Amurka za ta iya kawo karshen koriyar matukar ta ci gaba da barazanar farmakar yankinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.