Isa ga babban shafi
Spain

'Yan Catalonia 750,000 sun yi zanga-zanga a Barcelona

Akalla ‘yan yankin Catalonia dubu 750 ne suka gudanar da zanga-zanga, a birnin Barcelona, domin neman gwamnatin Spain ta saki jagororin yankin da har yanzu take tsare dasu, sakamakon rawar da suka taka wajen fafutukar neman ballewar yankin daga kasar.

Dubban 'yan Catalonia a birnin Barcelona sun kunna fitilar wayoyin hannunsu yayin zanga-zangar neman gwamnatin Spain ta saki jagororin yankin da take tsare da su. 11 ga Nuwamba, 2017.
Dubban 'yan Catalonia a birnin Barcelona sun kunna fitilar wayoyin hannunsu yayin zanga-zangar neman gwamnatin Spain ta saki jagororin yankin da take tsare da su. 11 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Albert Gea
Talla

A ranar 27 ga Oktoban da ya gabata, shugabannin yankin na Catalonia suka yi shelar ballewarsa daga Spain. Sai dai jim kadan bayan hakan, Fira Ministan kasar Mariano Rajoy ya tube shugaban yankin Carles Puigdemont daga mukaminsa, tare da rusa majalisar yankin, bayan tsare wadanda suka jagoranci fafutukar da dama.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar a makon da ya gabata, ya nuna cewa jami’yyu masu ra’ayin ‘yan aware ne zasu lashe mafi yawan yawan kuri’un da za’a kada, a sabon zaben yankin da za’a yi a watan Disamba mai zuwa, sai dai babu tabbacin zasu iya samun rinjayen da suke bukata na karfafa aniyarsu ta ballewa daga kasar Spain.

A makon da ya gabata babbar kotun Spain ta bada umarnin a kamo mata tsohon shugaban yankin Carles Puigdemont wanda ya tsere zuwa kasar Belgium tare da wasu ministocinsa bayan tube shi daga mukaminsa da Spain ta yi.

A halin yanzu Puigdemont ya mika kansa ga jami'an tsaron kasar Belgium, bayan umarnin mika mata shi da kotun kolin Spain ta bada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.