Isa ga babban shafi
Turai

Ƙudus-Ƙasashen Turai ba za su sauya matsaya ba

Shugabar ɓangaren kula da diflomasiyya na ƙasashen Turai Federica Mogherini ta ce ƙasashen ƙungiyar ba za su sauya matsaya a kan birnin Ƙudus ba duk da matakin da Amurka ta ɗauka.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da shugabar diflomasiyya ta EU Federica Mogherini a Brussels.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da shugabar diflomasiyya ta EU Federica Mogherini a Brussels. REUTERS/Francois Lenoir TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Federica ta yi wannan bayani ne sa'ilin ziyarar firaministan Isra'ila Benjamin Natenyahu, wanda ya je birnin Brussels domin tattaunawa da ministocin harkokin waje na ƙasashen.

'Mun yi amannar cewa hanyar kawai da za a iya samar da zaman lafiya kan rikicin Isra’ila da Falasɗinu ita ce ta samar da ƙasashe biyu, waɗanda za su yi amfani da Ƙudus a matsayin fadar gwamnati, ta yin la'akari da iyakar da ta wanzu kafin shekarar 1967'-in ji Mogherini

Ta kara da cewa wannan ce matsayar kasashen Turai, kuma za su cigaba da martaba matsayar ƙasashen duniya a kan Ƙudus har sai an warware matsalar da ta jibanci birnin.

Shi dai Natenyahu ya buƙaci ƙasashen na Turai ne da su amince da matakin Amurka na ayyana Ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.