Ana zargin Faransa da sakaci kan haƙƙin bil'adama
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi shugaban Faransa Emmanuel Macron da yin riƙon-sakainar-kashi ga kare haƙƙin bil’adama, musamman a kan abinda ya jiɓanci ƴan gudun hijira da kuma cin zarafin bil’adama a ƙasar China.
Wallafawa ranar:
Roth ya ce Macron ya bayar da fifiko a ɓangaren kasuwanci da yaƙi da ta’addanci a kan kare haƙƙin bil’adama.
A lokacin da yake tsokaci bayan fitar da rahoton ƙungiyar na shekara ta 2018, shugabanta Kenneth Roth ya zargi Macron da fuska-biyu a ɓangaren yaki da take hakkin bil’adama.
Ya ƙara da cewa yayin da shugaban na Faransa ke kokawa kan rufdugun da Rasha da Turkiyya ke yi a kan ƴan tawaye na ƙasar Syria, a gefe guda ya kawar da kansa a kan cin zarafin bil’adama da ke faruwa a China, da Masar da kuma jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu