Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta samar da sabon tsarin cinikayya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin haramta tsarin kasuwancin kayayyakin abinci a kasar da manyan kasuwanni ke mafani da shi, wajen bai wa kwastomomi damar amfana da shirin ka sai daya a baka daya kyauta.Macron ya ce nan gaba kadan zai kaddamar da sabon tsarin kasuwancin da zai faranta zukatan manoma dama kanana da matsakaitan 'yan kasuwa.

Wata kasuwar kayan lambu a Faransa, wadda ake saran sabon tsarin shugaban zai shafe ta matukar majalisar zartaswar ta amince tare da mayar da kudurin doka.
Wata kasuwar kayan lambu a Faransa, wadda ake saran sabon tsarin shugaban zai shafe ta matukar majalisar zartaswar ta amince tare da mayar da kudurin doka. THOMAS SAMSON / AFP
Talla

Matakin dai ya na kunshe cikin wani kuduri doka kan kayan abinci da noma, wanda gwamnatin Emmanuel Macron ta gabatarwa majalisar Zartaswar kasar.

Karkashin Dokar gwamnati za ta kara farashin kayayyakin abinci domin bai wa kananan manoma damar amfana yadda ya kamata wajen samun isassun kudaden shigar da amfanin gonar da suke nomawa, inda za’a haramtawa manyan kasuwanni zaftare farashin kayayyakin abincin da kashi 34.

Bincike ya nuna cewa kasar ta Faransa na kan gaba a harkokin noma idan aka kwatanta ta da takwarorinta na cikin kungiyar tarayyar turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.