Isa ga babban shafi
Birtaniya

Yanzu muka fara daukar mataki kan Rasha - Theresa May

Firaministar Birtaniya Theresa May ta ce korar jami'an Diflomsiyyar kasar 23 da Rasha ta yi a yau Asabar da kuma kulle ofishin yada al'adunta da ke kasar ba zai sauya matakin da suka dauka kan Rashan ba, bayan gano hannunta a kisan Serge Skripal.May ta ce nan da 'yan kwanaki kadan Birtaniyar za ta kara sanar da wasu tsaurara matakai kan Rashan don nuna mata munin abin da ta aikata.

Firaminstar Birtaniya Theresa May.
Firaminstar Birtaniya Theresa May. Reuters
Talla

A cewar Theresa May Birtaniya ba za ta amince da keta haddin al'ummarta ko kuma wanda ke karkashin kariyarta ba, a don haka dole ta dauki kwararn matakai.

Birtaniyar dai ta samu goyon bayan kasashen Faransa Jamus da kuma Amurka wadanda suka fito karara suka yi Ala wadai da matakin amfani da nau'in gubar ta Novichok mai tsananin hadari.

Tun a ranar 4 ga watan Maris din da muke ciki ne aka yi amfani da nau'in gubar a Novichok kan tsohon jami'in leken asirin Rashan Sergei Skripal dan shekaru 66 da 'yarsa Yulia 'yar shekaru 33 lokacin da suka je wani shagon siyayya a Salisbury, lamarin da yasa aka kaisu asibiti don basu kulawar gaggawa.

A ranar bakwai ga watan na Maris ne kuma jami'an tsaro suka tabbatar da amfani da nau'in gubar kan tsohon dan leken asirin na Rasha, yayinda a ranar 12 ga wata Theresa May ta ce akwai yiwuwar da hannun Rasha a yunkurin kisan, inda ta ce za ta tsananta bincike.

Sai dai kuma a ranar 13 ga wata kwana guda bayan wancan zargi, Rasah ta fito ta musanta hannunta a kisan inda ta ce a shirye ta ke ta taimakawa Birtaniya da dukkanin bayanan da ta ke bukata don gano wadanda ke da hannu a yunkirin kisan dama batun amfani da nau'in sabuwar gubar mai hadarin gaske.

Haka zalika kwanaki biyu bayan wannan batu, Rashan ta kara fitowa ta ce itafa bata da kimiyyar hada wata nau'in guba mai suna Novichok da ka iya hallaka mutum cikin gaggawa.

A ranar 14 ga watan na Maris ne kuma Birtaniyar ta ce ta tabbatar da hannun Rashan tare da daukar matakin korar jami'an diflomsiyyarta 23 daga cikin 59 da ke birtaniyar baya ga kwace wasu kwangiloli daga hannun Rashan da suka shafi gasar cin kofin duniya na 2018.

Bayan sanar da matakin ne kuma Rashan ta ce Birtaniya ta jira na ta matakin, yayinda kuma a washegarin ranar kasashen Faransa Jamus da Amurka suka mara baya ga Birtaniyar yayinda a bnagre guda itama kungiyar tsaro ta NATO ta ce dole a dauki kwakkawarn mataki ganin cewa rabon da ayi amfani da makamanciyar gubar kan harkokin tsaro tun bayan yakin duniya na biyu.

Zalika itama kungiyar tarayyar turai EU batun shi ne gagarumin abin da za ta tattauna yayin taron da zai gudana tsakanin ranakun 22 zuwa 23 ga watan na Maris.

A ranar Asabar 17 ga watan na Maris ne dai ita ma Rashan ta mayar da Martini ta hanyar korar jami'an birtaniyar 23 baya ga kulle Ofishin yada ilimi da al'adunta da ke kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.