Isa ga babban shafi
Faransa

Yajin aikin kamfanin sufurin jiragen kasa ya gurgunta lamurra a Faransa

Kungiyar Ma’aikatan kwadagon kamfanin jiragen kasar Fransa da suka tsunduma yajin aikin watanni uku a yau litanin, da kuma samu karbuwa sosai na hasashen cewa yajin aikin zai dagula al’amurran sufuri lokaci zuwa lokaci a kasar, al’amarin da ke matsayin babban kalubale ga shugaban kasar Emmanuel Macron da kuma shirinsa na son kawoi sauye sauye a kasar.

kanun jiragen kasa na kamfanin CNCF a Faransa
kanun jiragen kasa na kamfanin CNCF a Faransa Reuters
Talla

Ma’aikatan tsabtace gari da na bangaren makamashi suma ba a barsu a baya ba wajen tsunduma cikin yajin aikin, domin ganin an sakasu a cikin jerin sunayen ma’aikatan kwadago na kasa maimakon birane, bugu da karin yajin aikin na ci gaba da a bangaren da ya shifi sufurin jiragen sama, inda aka shiga rana ta 4 da tsundumar ma’aikatan kamfanin jiragen saman Air France cikin yajin aikin neman karin albashi.

Domin fuskantar wannan ayari na masu nuna rashin jindadi, musaman bangaren sufurin jiragen kasa, da suka tsaya haikan wajen kalubalantar sauye sauyen da gwamnati ta kudiri aniyar ci gaba da yiwa fanin sufurin jiragen kasa, ministan sufurin kasar uwargida Elisabeth Borne, ta ce a shirye gwamnati take ta saurari koke koken ma’aikatan ta hanyar tuntuba da tattaunawa.

Babbar Kungiyar kwadago ta CGT ta ce yajin aikin na yau ya samu karbuwa sosai, ta yadda ya haifar da tabarbarewar fanin sufurin jiragen kasa da akowace rana faransawa miliyan 4,5 ke dogara da shi wajen kaikawowarsu a ciki da wajen kasar.

A cewar kamfanin sufurin jiragen kasar SNCF Yanzu haka ma’ aikaci jirgin kasar 1 a cikin 3 ne ke yajin aiki, kimanin (34%) a yayin da matukan jirgin 3 kan 4 kimanin (77%), ke yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.