Isa ga babban shafi
Turai

Babban bankin Jamus zai sallami ma'aikantan sa da dama

Babban bankin Deutsche na Jamus ya ce zai sallami ma’aikatansa dubu 7,000 da doriya a kokarinsa na ganin ya maido da yawan ribar da yake samu duk shekara a baya.Bankin Deutsche na da yawan ma’aikata, 97000 da doriya, 66,000 daga ciki a nahiyar turai ciki harda 42, a Jamus.

Babban bakin Deutsche na kasar Jamus
Babban bakin Deutsche na kasar Jamus REUTERS/Kai Pfaffenbach/Files
Talla

Sauran sassan da bakin ke da dubban ma’aikata sun hada da nahiyar Asiya, inda bankin ke da ma’aikata 21,000 da kuma Amurka mai kunshe da ma’aikatan bankin na Deutsche 10,000.

Zuwa karshen watan fabarairu da ya gabata bankin ya bada rahoton tafka asarar euro milyan 500, a shekarar da ta gabata. Zalika hannun jarin bankin na Deutsche ya ragu daga euro 91 a shekarun 2007 da 2008 zuwa euro 17 a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.