Isa ga babban shafi
Faransa-Angola

Shugaba Joao Lourenco na Angola na ziyarar aiki a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakuncin takwaransa na Angola João Lourenço a fadarsa ta Elysees. Wannan ne dai karo na farko da shugaban na Angola ke kai ziyarar aiki a Faransa, tun lokacin da aka zabe shi a watan satumbar shekarar da ta gabata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Angola Joao Lourenco yayin ziyarar aikin da shugaban na Angola ya fara yau a Faransa.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Angola Joao Lourenco yayin ziyarar aikin da shugaban na Angola ya fara yau a Faransa. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Bayan ganawarsu a gaban manema labarai, daga nan kuma shugaban na Faransa ya shiryawa bakonsa liyafar cin abincin rana, kafin daga bisani shugabannin biyu su sanya hannu kan yarjeniyoyi a fannoni da dama tsakanin kasashensu.

Daga cikin yarjeniyoyin har da ta tsaro da kuma bunkasa harkar noma, a daidai lokacin da Angola kasa ta biyu da ta fannin fitar da man fetur a Afrika ke kokarin fadada fannonin samun kudaden shiga a maimakon dogaro da mai.

Har ila yau bayanai na nuni da cewa shugabannin biyu sun tattauna kan sauran baututuwa da suka shafi nahiyar Afirka, musamman rikicin siyasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, wanda Faransa ke fatan ganin Angola ta taka muhimmiyar rawa domin warware wannan rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.