Isa ga babban shafi
Faransa

Ku daina tuhuma ta, inji tsohon shugaban Faransa Nicolas Serkozy

Tsohon Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, ya bukaci kotu ta jingine tuhumar da aka yi masa ta karbo makudan kudade daga hambararren shugaban kasar Libya Mu’ammar Gaddafi domin yakin neman zabensa na 2007 da bai yi nasara ba.

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da ke fuskantar zarge-zargen badakalar cin hanci da rashawa.
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da ke fuskantar zarge-zargen badakalar cin hanci da rashawa. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

A ranar 21 ga watan maris da ya gabata ne, kotun ta sanar da wannan zargi a kan tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy, to sai dai a ranar larabar da ta gabata, lauyan da ke kare shi Thierry Herzog ya shigar da bukatar ganin an soke tuhumar saboda abinda ya kira rashin hujjojin da ke tabbatar da cewa tsohon shugaban ya karbin kudaden yakin neman zaben daga Gaddafi.

Tun dai bayan faduwar gwamnatinsa ne Nicolas Sarkozy ya shiga wani hali na koma baya a harkokin siyasar sa, abinda ya nuna yadda farin jininsa ke dada raguwa, a yayin da hukumomi a kasar ta Faransa suka tuhumi wasu manyan jami'an gwamnatin Sarkozy da mara wa kokarin amsar manyan kudade daga kasar Libya domin yakin neman zabensa.

Abin kunya ne ga shugaba irinna faransa ya karbi kudi daga wata kasa da sunan taimako don gudanar da wasu hidindimmu nashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.