Isa ga babban shafi

Macron ya goyi bayan ladabtar da kasashen EU kan bakin-haure

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya goyi bayan kakaba takunkumin karya tattalin arziki kan duk wata kasa da ke cikin kungiyar trayyar turai da ta karbar bakin-haure.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin karbar bakuncin Fira ministan Spain Pedro Sanchez a fadar Élysée da ke birnin Paris, ranar 23 ga watan Yuni, 2018.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin karbar bakuncin Fira ministan Spain Pedro Sanchez a fadar Élysée da ke birnin Paris, ranar 23 ga watan Yuni, 2018. AFP /© Ludovic Marin
Talla

Macron ya bayyana haka ne yayin jawabi ga manema labarai tare da sabon Firaministan Spain Pedro Sanchez a birnin Paris, wanda ya kai masa ziyara a yau Asabar.

Shugabannin biyu sun kuma amince da gina wasu sabbin cibiyoyin ajiye bakin-hauren da ke dakon hukumomin kasashen turan da suke son shiga su tantance bukatarsu ta neman mafaka.

Taron shugabannin na Spain da Faransa ya zo ne sa'o'i bayan da jami’an tsaron gabar ruwa na Spain suka sake ceto bakin-haure akalla 418, a wani gagarumin aikin da suka gudanar a yau Asabar.

Ma’aikatar ayyukan ceton Spain ta ce aikin ceton ya gudana ne a mashigin ruwan Gibralta, inda aka ceto mutane 262 da ke cikin jiragen ruwa 15, sai kuma wasu bakin-hauren 129 da aka ceto a tsakanin tsibirin Canary da Tekun Atlantic.

Karin bakin-haure 27 kuma, jami’an na Spain sun ceto su ne a tekun Meditterranean, a yankin ruwan da ke tsakanin kasar ta Spain da kuma Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.