Isa ga babban shafi

Al'ummar Mexico na jefa kuri'a a zaben shugaban kasa

Yau lahadi al’ummar Mexico ke kada kuri’a a zaben shugabancin kasar, wanda wata kuri’ar jin ra’ayi da aka yi gabannin zaben, ta nuna dan takara mai kishin kasa Andres Manuel Lopez Obrador na jam’iyyar Morena ke kan gaba wajen karbuwa.

Dan takarar shugabancin Mexico mai ra'ayin kishin kasa, Andres Manuel Lopez Obrador na jam'iyyar (MORENA), yayin jawabi ga magoya bayansa a birnin Mexico City.
Dan takarar shugabancin Mexico mai ra'ayin kishin kasa, Andres Manuel Lopez Obrador na jam'iyyar (MORENA), yayin jawabi ga magoya bayansa a birnin Mexico City. REUTERS/Henry Romero
Talla

Zaben shugabancin Mexico ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan kasar suka kosa da mulkin jam’iyyu mafiya girma a kasar, wato PRI wadda ke mulki da kuma PAN ta ‘yan adawa, wadanda suka mulki kasar har na tsawon kusan shekaru 100.

Mexico ta shafe tsawon lokaci tana fama da matsalar karfafan kungiyoyin masu safarar kwayoyi kana dayawaitar kisan gilla, la’akari da wata kididdiga da ta nuna cewa a shekarar 2017 da ta gabata kadai, an hallaka mutane akalla 25,000 ta hanyar kisan gilla.

Ko a ranar Asabar da ta gabata, kwana guda kafin zaben na yau, sai da wasu 'yan bindiga suka hallaka wani dan jarida a jihar Quintana Roo da ke kudancin kasar ta Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.