Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya amsa laifin da dogarinsa ya aikata

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shaida wa 'yan majalisun dokokin kasar da ke cikin jam'iyyarsa cewa, ya amsa laifin da babban dogarinsa, Alexandre Benalla  ya aikata na dukan wani mai zanga-zanga, yayin da Macron ya bayyana matakin dogarin a matsayin yaudara.  

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da babban dogarinsa, Alexandre Benalla
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da babban dogarinsa, Alexandre Benalla 路透社
Talla

Wannan na zuwa ne bayan shugaba Macron ya sha caccaka daga bangaren 'yan adawa kan rashin cewa komai game da wannan badakala da ta rura wutar siyasar kasar.

Ko a ranar Talata sai da shugaban ma'aikatan fadar Macron, Ptrick Strzoda ya gurfana a gaban Majalisar Dokokin Kasar kan wannan badakala

Strzoda, ya shaida wa kwamitin bincike na majalisar cewa, shi kadai ne ya dauki matakin dakatar da  Benalla daga aiki sakamakon ganin hoton bidiyon da ke nuna yana dukan masu zanga-zanga a birnin Paris.

Da aka tambaye shi ko meye dalilinsa na kin gabatar da zancen a gaban shari’a maimakon daukan mataki na gaban kansa, sai Strzoda ya ce ya yi hakan ne a matsayinsa na shugaba ga wanda ake tuhamar.

Har ila shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasar ya ce, tabbas yana da masaniya a game da kasancewar Benalla tare da ‘yan sanda da aka tura wurin wannan zanga-zanga da aka yi ranar 1 ga watan Mayu.

Strzoda ya ce, jami’in ya sanar da shi cewa, ya halarci wurin sakamakon samun goron gayyata daga rundunar ‘yan sandan birnin Paris domin sa ido a lokacin tarzomar, kuma wani babban jami’i a rundunar ‘yan sandan mai suna M Simon ne ya gayyace shi a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.