Isa ga babban shafi
Faransa

Wasu kasashen Turai sun shawarci yan kasar su da su dakata da ziyarar Faransa

Wasu kasashen Turai da suka hada da Belgimu da kasar Tcheque sun yi kira zuwa yan kasar su da su kaucewa zuwa Faransa, inda yanzu haka ake sa ran masu zanga-zanga sanye da riguna masu kalar dorowa za su banzama saman tituna.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin Paris
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin Paris REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Hukumomin Faransa sun dau tsatsauran matakan tsaro domin dakile duk wata barazana da kan iya kuno kai dama haifar da rudani a fadin kasar inda aka sanar da baza kusan jami’an tsaro dubu 90 da suka hada da yan Sanda da Jandarmomi.

Wasu rahotannin baya bayan nan na nuni cewa Firaministan kasar Edouard Philippe ya samu ganawa da wasu wakilan masu zanga-zanga a fadar sa da zimar cimma matsaya domin kawo karshen tarzomar da aka share wata daya ana yi a kasar ta Faransa.

A fitowar yau asabar yan sanda sun kama kusan masu zanga-zanga 278.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.