Isa ga babban shafi
Faransa-Zanga-Zanga

Jami'an tsaron Faransa sun kame masu zanga-zanga kusan 2000

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ta tabbatar da kame akalla mutane dubu 1 da dari 723 cikin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ke juyewa zuwa rikici tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

Arangamar tsakanin Jami’an tsaron da Masu Zanga-zangar wadda ita ce mafi muni cikin fiye da shekaru 10 da Faransa ke fuskanta, ta kai ga harba hayaki mai sanya hawaye kan dandazon jama’ar don tarwatsa su.
Arangamar tsakanin Jami’an tsaron da Masu Zanga-zangar wadda ita ce mafi muni cikin fiye da shekaru 10 da Faransa ke fuskanta, ta kai ga harba hayaki mai sanya hawaye kan dandazon jama’ar don tarwatsa su. CHARLY TRIBALLEAU / AFP
Talla

Cikin bayanan da ma’aikatar ta fitar yau Lahadi, ta ce daga cikin adadin kusan dubu biyun da aka kame kimanin dubu 1 da dari 2 da 20 na gidan yari yanzu haka wadanda ake zargi da tayar da hankali da kuma kone-kone a jiya Asabar, yayinda sauran za a iya sakinsu bayan lafawar rikicin.

Ministan harkokin cikin gida Minister Christophe Castaner ya ce kimanin mutane dubu 136 ne suka shiga zanga-zangar yau, bayan arangamarsu da jami’an tsaro a jiya Asabar, inda ya ce matukar suka ci gaba da kone kone tare da lalata dukiyoyin jama’a babu shakka za su ci gaba da kame su har su zuwa lokacin da za su saduda.

Da yammacin jiya Asabar ne dai Mr Castaner ya ce an samu lafawar zanga-zangar bayan kara yawan jami’an tsaro musamman a birnin Paris gab da fadar shugaban kasa ta Elysee wajen da masu zanga-zangar suka yiwa kawanya.

Arangamar tsakanin Jami’an tsaron da Masu Zanga-zangar wadda ita ce mafi muni cikin fiye da shekaru 10 da Faransa ke fuskanta, ta kai ga harba hayaki mai sanya hawaye kan dandazon jama’ar don tarwatsa su.

Dubban masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin dai na ci gaba da bore ne tare da neman lallai shugaban kasar Emmanuel Macron ya sauka daga mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.