Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Kungiyar EU ta maka Birtaniya a kotu

Hukumar Tarayyar Turai ta shigar da karar Birtaniya a gaban kotun kolin nahiyar bisa zargin ta da karya dokokin harajin kayayyakin masarufi, a daidai lokacin da ya rage watani biyu kasar ta kammala ficewa daga Turai.

Firaministar Birtaniya Theresa May na cikin tsaka mai wuya dangane da kulla yarjejeniyar ficewar kasar daga gungun kasashen Turai
Firaministar Birtaniya Theresa May na cikin tsaka mai wuya dangane da kulla yarjejeniyar ficewar kasar daga gungun kasashen Turai REUTERS/Francois Lenoir/File Photo
Talla

Hukumar Tarayyar Turai ta ce, ta dauki matakin ne saboda yadda Birtaniya ta fadada tsarinta na kin karabar haraji kan wasu kebantattun kayakkain masarufi da tun asalin ba sa cikin karkashin dokar da aka kwashe gomman shekaru ana amfani da ita.

Daukan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake shakku kan makomar Firaminista Theresa May kan fafutukarta ta neman goyon baya game da yarjejeniyar ficewar da ta cimma da Tarayyar Turai, yayin da a gefe guda, take kokarin kauce wa raba gari da EU ba tare da cimma wata matsaya ba kafin nan da ranar 29 ga watan Maris.

Yanzu haka dai, ya zama dole Birtaniya ta amsa kiran kotun, lura da cewa, ba ta kammala ficewa daga gungun kasashen Turan ba.

Kwamishiniyar ayyuka ta EU, Marianne Thyssen ta ce, za a hukunta Birtaniya kamar yadda za a hukunta duk wani mamban da ya karya doka a gungun kasashen Turai, domin kuwa har yanzu kasar na karkashin kungiyar ta EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.