Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta soki Italiya kan yin katsalandan a harkokinta

Kiran jakadan Faransa dake Italiya gida na tamkar busar usur din hutun cin abinci ne, bayan katsalandan a cikin harakokin cikin gidan faransa da mahukumtan Italiya suka yi, in jin ministan dake kula da harakokin turai ta kasar Fransa Nathalie Loiseau.

Nathalie Loiseau ministar dake kula da harakokin turai
Nathalie Loiseau ministar dake kula da harakokin turai Philippe LOPEZ / AFP
Talla

A cikin wata fira da tashjar radio Classique ministan Nathalie Loiseau.ta ce kiran jikadan gida bai kamata ba a yi masa mummunar fahimta, tamkar kiran hutun cin abinci ne a illa iyaka.

Sai dai ta kara da cewa al’amarin da ya faru bai yi ba, ta yadda wani mambar gwamnatin wata kasa ta ketare zai shigo Faransa ya nuna goyon bayansa ba wai ga shugaban siyasa ba, a a ga wanda ke kiran kaddamar da yakin basasa, da kuma ke kiran a kifar da shugaban kasa da gwamnati, wannan abin takaici bai taba faruwa ba a tarihi.

A cewar ministar wannan katsalandan wani, mummunan al’amari ne da mutanen dake kiran kansu shuwagabani, da ke cewa burinsu shine kare muradun italiya suka aikata

Ganawar da aka yi ta ranar talatar da ta gabata tsakanin mataimakin Firayi ministan Italiya Luigi Di Maio, da masu sanye da ruwan dorowar rigunan da suka share makwanni suna da zanga zangar nuna kin jinin shugaba Emmanuel Macron.

a wurin mahukumrtan paris babbar tsokana ce a diflomasiyance da kuma ta yi muni sosai tsakanin kasashen 2 da suka share tsawon watanni suna kai ruwa rana

Da aka tambayeta ko tsakanin Paris da Rome wa keda alhakin faruwar lamarin, uwargida Loiseau ta ce, ai bas ai an fada ba faransa ce ke da gaskiya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.