Kasa da kashi 5 na 'yan gudun hijira ne kadai ke samun matsugunai - MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasa da kashi 5 na baki 'Yan gudun hijira ne suka samu matsugunai a kasashen Yammacin duniya a shekarar 2018, sakamakon matakin da Amurka ta dauka na rufe kofofin ta wajen karbar irin wadanan mutane.
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da Yan gudun hijira ta Majalisar ta ce Amurka ta karbi baki dubu 17,113 bara, matakin da ya sanya ta a sahun gaba, yayin da wasu kasashe 27 suka karbi baki dubu 55,692 a karkashin shirin hukumar.
Sai dai alkaluman da Amurkar ta karba ya gaza dubu 24,559 da ta karba a shekarar 2017, yayin da a shekarar 2016 kasar ta karbi baki 78,761.
Kasar Canada ce kasa ta biyu da tafi karbar baki, inda a bara ta karbi dubu 7,713 sai kuma Birtaniya a matsayi ta 3 da dubu 5,702 sai kuma Faransa a matsayin na 4 da dubu 5,109.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu