Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

May na neman goyon bayan Merkel da Macron kan karin wa'adin Brexit

Firaministar Birtaniya Theresa May yanzu haka na wata ganawa da takwarorinta na Faransa da Jamus don tattaunawa kan bukatar kara mata wa’adin ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, gabanin taron kungiyar gobe Laraba a Brussels.

Firaministar Birtaniya Theresa May yayin ziyarar da ta kai Jamus don ganawa da Angela Merkel a Berlin
Firaministar Birtaniya Theresa May yayin ziyarar da ta kai Jamus don ganawa da Angela Merkel a Berlin REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Yayin ganawar ta Theresa May da Angela Merkel, ganawar da May da kanta ta yi tattaki zuwa birnin Berlin na Jamus, Firaministar ta nemi goyon bayan Merkel wajen ganin EU ta amince da kara mata wa’adin ficewa a karo na biyu daga ranar 12 ga watan nan kamar yadda ta nema da farko zuwa 30 ga watan Yuni mai zuwa.

Theresa May wadda daga ita har Angela Merkel suka gaza cewa uffan ga manema labarai bayan ganawar ta sa’o’i biyu, kai tsaye ta nufi birnin Paris na Faransa inda a nan ma ake saran ta mika makamanciyar bukatar ga shugaba Emmanuel Macron sai dai akwai alamun da wuya shugaban na Faransa ya mara baya ga bukatar ta May.

Firaministar ta Birtaniya dai na fatan taron gaggawa na kungiyar EU da zai gudana a gobe Laraba, ya amince da matakin kara mata wa’adin ficewar zuwa nan da watanni biyu masu zuwa, dai dai lokacin da ta ke ci gaba da tattaunawa da banagren adawa don ganin Birtaniyar ta samu sukuni fita daga EU tare da cikakkiyar yarjejeniya.

A bangare guda yayin wani taron ministocin harkokin kasashen Turai a Luxembourg, kai tsaye ministan Jamus Micheal Roth da na Faransa Amalie de Montchalin sun caccaki matakin kara wa’adin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.