Isa ga babban shafi
Faransa-haraji

Sabon tsarin zaftare haraji zai tallafawa talakawan Faransa- Macron

Gwamnatin Faransa ta ce sabon tsarin rangwamin haraji da ta bullo da shi zai taimakawa masu karamin karfi, haka zalika ba zai samar da gibi a kasafin kudin kasar ba, ka na kuma zai saukaka yawan kudin da ake kashewa.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa @AFP
Talla

Cikin jawaban da ya gabatar, Shugaba Emmanuel Macron ya sha alwashin rage harajin da darajarsa ya kai Yuro biliyan 5, a wani martani ga zanga zangar watanni 5 da masu sanye da rigunar dorawa ke ciki, sakamakon abin da suka kira matsin rayuwa a Faransa.

Ministan kudi da tattalin arziki na Faransa, Bruno Le Maire ya ce, gidajen iyalai miliyan 15 ne za su amfana da wannan sabon tsarin, wanda ke tattare da rangwamin haraji baya ga karin albashi da ya kai yuro biliyan 10 kamar yadda aka sanar a watan Disamba.

Daga cikin matakan da za a dauka don cike gibin da wannan rangwame zai samar ba tare da ya shafi tattalin arzikin kasar ba, har da rage yawan kudin tafiyar da gwamnati, wanda shi ne babban kalubalen shugaba Macron.

Emmanuel Macron ya yi bayanin cewa mai yiwuwa a rage wasu daga cikin hukumomin gwamnati, tare da sauyawa wasu ma’aikatan gwamnati wuraren aiki daga Paris zuwa wasu yankunan kasar.

A cewarsa an shirya tsaf don yin wannan rangwami na haraji, inda za a toshe duk wata kafa da kamfanoni ke bi wajen kauce wa haraji, a kwadaita wa al’umma kara azama wajen aiki, da kuma rage rashin aikin yi, wanda ke kara tsananta karkashin gwamnatin Emmanuel Macron.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.