Isa ga babban shafi
Turai

Faransa da Jamus sun kasa cimma matsaya a taron EU

Da kammala zaben Majalisar dokokin Turai, shugabannin kasashen yankin sun kasa cimma matsaya don fitar da sunan shugaban kungiyar ta Turai.Faransa da Jamus, kowanen su na da nasa dan takara, yanayin da ya haifar da tsaiko a wannan zama.

Angela Merkel Shugabar Gwamnatin Jamus da Emmanuel Macron  a taron EU
Angela Merkel Shugabar Gwamnatin Jamus da Emmanuel Macron a taron EU 路透社。
Talla

Shugabannin kasashen yankin Turai a wannan taro na jiya talata sun kasa fitar da sunan wanda za a nada a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta Turai, mukamin da Jean-Claude Juncker ke rike da shi yanzu haka.

Karkashin dokokin hukumar Turai, shugabannin kasashen yankin 28 ne ke zaben shugaban hukumar, kafin daga bisani a gabatar da sunansa gaban majalisar dokoki mai wakilai 751 domin ta tabbatar da shi.

Shugabanin Faransa da Jamus sun kasa cimma matsaya don fitar da sunan wanda ya dace,yayinda Shugaban kwamity zartarwa Donald Tusk ya bayyana cewa bai dace an fuskanci irin wannan tsaiko ba.

A halin yanzu dai mataimakin Juncker wanda ya fito daga jam’iyyar masu tsaka-tsakan ra’ayi kuma tsohon minista daga kasar Netherland Frans Timmermans, ne Faransa ke fatan gani ya samu wannan kujera,yayinda Jamus ta bakin waziyar kasar Angela Merkle ta gabatar da sunan Manfred Weber.

Shugaban Faransa ya bayyana cewa wanda ya dace ya rike wannan mukami shine mutumen da keda sanin matuka dangane da siyasar yankin da kuma zai iya taka gaggarumar rawa don kare muradun kasashen nna Turai.

Ana sa ran Shugabanin kasashen za su cimma matsaya kafin babban taron kasashen Turai kama daga ranaku 20 zuwa 21 na watan yuni,lokacin da za a sanar da sunan sabon Shugaban hukumar ta Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.