Isa ga babban shafi
Faransa

Yajin aikin sufuri a Faransa na shirin shiga mako na 4

Gwamnatin Faransa da hadakar kungiyoyin ma’aikatan sufuri na takaddama kan bangaren da ke da alhakin haddasawa al’ummar kasar matsin rayuwa sanadiyyar yajin aikin bangaren sufurin na fiye da makwanni 3 da ya dakushe harkokin tafiye-tafiye musamman a lokacin bikin Kirsimeti.

wata tashar jiragen kasa a Faransa.
wata tashar jiragen kasa a Faransa. RFI/Tiếng Việt
Talla

Takaddama tsakanin hadakar kungiyar Sufurin ta Faransa da bangaren gwamnati na zuwa a dai dai lokacin da ake fatan kawo karsehn yajin aikin wanda kawo yanzu aka shafe fiye da makwanni 3 ana yi, ko da dai gwamnatin ta nuna kin amincewa da samar da sauyi a sabuwar dokar fanshon da ritaya.

A wata zanatawarsa da manema labarai mataimakin ministan sufurin Faransa Jean-Baptiste Djebbari ya zargi kungiyar ma’aikatan sufurin kasar ta CGT da kalubalantar duk wani shirin gwamnati na samar da sauye-sauye, yayinda a bangare guda shima shugaban kungiyar Philippe Martinez ya zargi gwamnatin da haddasa yamutsi da ke jefa al’umma cikin wahala.

Yajin aikin na Faransa da yanzu ke shiga kwana na 26 dai ya dara na shekarar 1995 da aka shafe kwanaki 22 ana yi yayinda ya ke neman tarar kere yajin aiki mafi tsawo da kasar ta taba fuskanta wato na karshen shekarar 1986 da ya kai har farkon 1987.

Ko yammacin jiya lahadi dai, ilahirin tashoshin jiragen kasa masu matukar gudu da ke sada al’umma da sassan kasar ta Faransa sun ki gudanar da aiki inda suka kulle tashoshinsu, yayinda ake ganin daidaikun jiragen kasa da kuma motocin sufuri da jigilar jama’a.

Bangaren gwamnatin da kungiyar ma’aikatan sufurin dai sun alkawarta zama a ranar 7 ga watan Janairu don dinke barakar da ke tsakaninsu duk da dai kowanne bangaren ya ja tunga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.