Isa ga babban shafi
Bosnia

Kwamandan sojin Bosnia na shakkun samun adalci a kotun Duniya

Lauyoyin tsohon babban hafsan sojin Sabiya, Ratko Mladic, sun shaida wa kotun Majalisar Dinkin Duniya a yau Talata cewa, tsohon hafsan na kokwanton samun adalci saboda baya cikin natsuwar da har zai bayyana a sauraron bahasi, a daukaka karar hukuncin daurin rai da rai da aka yanke mai a game da aikata kisan kare dangi.

Ratko Mladic tsohon kwamandan sojin Bosnia
Ratko Mladic tsohon kwamandan sojin Bosnia REUTERS/Martin Meissner
Talla

Mladic, mai shekaru 78, wanda ake wa lakabi da ‘Mahaucin Bosnia’ ya kalubalanci hukuncin daurin rai da rai da aka yanke mai, a kan aikata laifin kisan kare dangi, laifukan yaki da cin zarafin bil adama a yakin basasar tsohuwar Tarayyar Yugoslavia, har ma da kisan kare dangi na yankin Srebrenica a shekarar 1995.

Amma lauyoyinsa sun ce suna halartar kotun ne cikin korafi, duba da yadda aka fara shari’ar kwanaki biyun bayan da alkalai suka yi watsi da bukatar a dage zaman kotun har sai an sake yi wa wanda suke karewa gwajin tantance lafiyarsa.

Mladic ya bayyana a gaban kotun a yankwane, sanye da mayanin fuska duba da yanayi na annobar coronavirus da ake ciki, amma daga bisani ya bude fuskar tasa.

An dage sauraron daukaka karar sau da dama tun daga watan Maris saboda aikin tiyata da likitoci suka mai, ga kuma bullar annobar COVID 19.

A shekarar 2011 aka kama Mladic, aka kuma yanke mai hukuncin daurin rai da rai, bisa hannu da yake da shi a kisan kare dangi mafi muni a Turai a tsakanin shekarun 1992 zuwa 95, inda Musulmi dubu 8 suka rasa rayukansu a Bosnia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.