Isa ga babban shafi
Macron-EU

Macron ya bukaci gaggauta mayar da Majalisar Turai Strasbourg

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Majalisar dokokin Turai da ta koma muhallinta da ke birnin Strasbourg cikin kankanin lokaci, bayan mayar da zaman ta Brussels sakamakon barkewar cutar korona.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Lewis Joly / AFP
Talla

Yayinda ya ke jawabi ga dalibai a Lithuania, Macron ya ce muddin suka amince da cigaba da zaman Majalisar a Brussels toh an gama da su, domin kuwa nan da shekaru 10 masu zuwa komai zai koma Brussels, kuma hakan ya saba da manufar kungiyar Turai.

Shugaban Majalisar David Sassoli ya ce 'yan Majalisun ba za su koma Strasbourg ba a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.