Isa ga babban shafi

Faransan zata ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki har karshen shekara - Le Maire

Minstan Kudin Faransa Bruno Le Maire ya bayyana cewa kasar zata fuskanci mummunar komabayan tattalin arziki har zuwa karshen wannan shekara ta 2020, sabo da matakan kiriya daga coronavirus da ta sake bulla a karo na biyu, a dai-dai lokacin da Hukumar kididdigar Farasa ke cewa tattalin arzikin kasar ya fadi da kashi 18, yanzu haka saboda halin da kasar ke ciki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Ludovic Marin/Pool
Talla

Wannan na zuwa ne a dai-dai laokacin da kayayyakin masarufi da Faransa ke samarwa suka fara fuskantar koma baya a kasashen yankin Golf, da suke da karbuwa da wata daraja ta musamman a baya.

Sakamakon nuna bacin rai da kasashen musulmai suka nuna tare da kiran kauracewa kayayyakin na Faransa, bayan da shugaban kasar Emmanuel Macron ya kare masu zanen bataci ga annabi Mohammadu mai tsari da amincin Allah su tabbata a gareshi.

A Kuwait, manyan shaguna 60 suka fitar da kayayyakin Faransa, yayin da wasu kamfanonin shirya tafiye-tafiye suka dakatar da Farasa daga cikin jerin kasashen da ake ziyarta.

Khalid Hussain manajan daya daga cikin shuganun da suka kauracewa kayayyakin Faransar, ya shaidawa AFP cewar sunyi haka ne, soboda taba Annabi, kololuwar tsokana da za’ayi wa addini kenan.

A kasar Qatar ma, Al-Meera, wani babban kamfani dake rarrabawa manyan shuganu kayayyaki ya dakatar da na Faransa cikin kayayyakinsa, yayin da

Wasu majiyoyi biyu na gwamnati suka shaidawa AFP cewar, Qatar za ta kaurace wa taron tattaunawar zaman lafiya da Paris zata karbi bakwanci ranar 11 ga watan Nuwamba.

Haka batun yake a kasar Saudiya da Hadeddiyar Daular Larabawa da sauransu…

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.