Isa ga babban shafi
Romania

Masu Shekaru 18 Zuwa 55 Ne Za Su Sami Alluran Rigakafin Corona A Romania

Hukumomin kasar Romania , a yau Asabar suka karbi kason farko na maganin rigakafin kwayar cutar AstraZeneca, kuma Mahukuntan sun ce za’a yi amfani da shi ne kawai kan masu shekaru tsakanin 18 zuwa 55 a duniya.

Tambarin Kamfanin magungunan AstraZeneca
Tambarin Kamfanin magungunan AstraZeneca REUTERS
Talla

Romania ta shiga sahun wasu kasashen duniya da suka takaita amfani da wannan magani, duk da cewa kungiyar kasashen Turai na cewa ana iya amfani da wannan magani kan kowa da kowa.

Kason farkon da kasar Romania ta samu ya kai sunki dubu 81,600.

AstraZeneca ya kasance magani na uku da Kungiyar Tarayar Turai ta amince ayi amfani da shi a Turai bayaga magungunan Pfizer/BioNTech da kuma Moderna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.