Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar dokokin Faransa ta amince da dokar yaki da tsatsauran ra'ayin Islama

Majalisar Wakilan Faransa ta kada kuri’ar amincewa da kudirin dokar yaki da tsatsauran ra’ayin Islama da gwamnatin kasar ta aike mata a matsayin martani ga kungiyoyin addinin da ke yunkurin yin karan tsaye ga matsayin kasar na wacce ba ruwanta da addini.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Thibault Camus/Pool via REUTERS
Talla

Kudirin dokar wanda aka caccaka bisa zargin cewa wani yunkuri ne na shafa wa Musulmi kashin kaji da kuma bai wa kasar karfin dakile yancin fadin albarkacin baki, da na gudanar da kungiyoyin addini ya samu goyon bayan akasarin ‘ya majalisar dokokin.

Jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron ce ta yi kane kane a kan dokar, inda wakilai 347 suka goyi bayanta, yayin da 151 suka zabi akasi, 65 suka kaurace.

Yanzu za a mika wa majalisar dattijan kasar daftarin dokar, inda nan ne gizo ke saka, duba da cewa jam’iyya mai mulki ba ta da rinjiye.

A sakamakon damuwar da gwamnatin Faransa take nunawa a a game da kudaden tafiyar da masalatai da ke shigowa daga kasashen Qatar, Turkiya da Saudiyya, dokar ta bukaci kungiyoyin addini su rika bayyana dimbin kudaden da suke samu a matsayin gudumawa daga kasashen waje.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye shiryen tinkarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa,

Kusan mutane 200 ne suka gudanar da zanga zangar adawa da kudirin dokar, su na mai zargin cewa zai karfafa cin zarafin Musulmai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.