Isa ga babban shafi
Myanmar

Majalisar Dinkin Duniya ta sake caccakar gwamnatin sojin Myanmar bayan mutuwar mutane biyu

Mutuwar wasu mutane 2 masu zanga zangar adawa da hambarar da gwamnati a Myanmar ta sake janyo kakkausar suka daga Majalisar Dinkin Duniya a Lahadi, a yayin da masu makoki ke shirin bison wata budurwa da ta mutu sakamakon raunin da ta samu daga harbin bindiga a lokacin gangamin nuna rashin amincewa da masu juyin mulkin.

Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya. RFI
Talla

Sannu a hankali hukumomin kasar sun zafafa matakan da suke dauka a kan masu zanga zangar lumana da ke neman a maido da jagorar farar hular Aung San Suu Kyi kan karagar mulki.

A jiya Asabar ne lamarin ya fi mununana, a cikin makonni 2 na zanga - zangar gama – garin, inda jami’an tsaro suka bude wa gungun masu gangami wuta a birnin Mandalay, lamarin da ya tsorata jama’a, suka shiga arcewa.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki hukumomin yankin sakamakon abin da ya kira ‘amfani karfi fiye da kima’, wanda masu aikin agaji suka ce ya yi sanadin mutuwar wani matashi, tare da raunata gwammai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.