Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Faransa ta fadada dokar takaita walwala zuwa karin yankunan kasar

Gwamnatin Faransa ta bayyana takaita zirga zirgar jama’a a arewacin yankin Calais daga karshen wannan mako domin dakile yaduwar cutar korona, yanki na 3 da irin wannan mataki ya shafa.

Firaministan Faransa Jean Castex
Firaministan Faransa Jean Castex AP - Francois Mori
Talla

Firaministan kasar Jean Castex yace samun mutane sama da 400 da suka kamu da cutar daga cikin ko wadanne mutane 100,000 ya sa Yankin Calais ya kusa ribanya adadin mutanen dake kamuwa da cutar a fadin kasa.

Saboda haka daga ranar asabar dokar zata fara aiki da karfe 8 na safe zuwa karfe 6 na yammacin lahadi, yayin da dokar hana fitar dare daga karfe 6 na yamma ke cigaba da aiki a fadin kasar.

Tun daga watan Janairu, gwamnatin shugaba Emmanuel Macron na kokarin ganin dakile yaduwar cutar daga yanki zuwa yanki, sabanin matakan da kasashe makota irin su Birtaniya ke dauka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.