Isa ga babban shafi
Faransa-Lafiya

Faransawa sun soma kokarin samar da rigakafin kwayar cutar HIV

Karon farko cikin shekaru sama da 10, kwararru a Faransa sun sake yunkurawa wajen kokarin samar da rigakafin hana kamuwa da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV.

Hoton dake nuna yadda kwayar cutar HIV ta yi illa ga wasu kwayoyin hallitar jikin dan adam.
Hoton dake nuna yadda kwayar cutar HIV ta yi illa ga wasu kwayoyin hallitar jikin dan adam. © Credit: NIAID. License: CC BY 2.0.
Talla

Jaridar France Info tace cikin watan Afrilu mai zuwa tawagar kwararrun da ke kokarin samar da rigakafin na HIV za ta kaddamar da Shirin gwajin maganin kan mutane.

A ranar Alhamis 25 ga watan Fabarairu, kwararrun dake karkashin jagorancin Farfesa Yves Levy, suka yi shelar neman mutane 72 da za su sadaukar da kansu wajen gwajin rigakafin na HIV.

Yunkuri na karshe da aka yi wajen samar da maganin cutar mai karya garkuwar jiki dai shi ne na cikin shekarar 2009, sai dai kwararru a waccan lokacin basu samu nasara ba, domin tasirin kasha 30 cikin 100 kawai rigakafin ya y ikan cutar ta HIV.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.