Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai-Covid-19

Tarayyar Turai za ta maka kamfanin AstraZeneca kotu kan saba yarjejeniyar

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce nan ba da jimawa ba zata gurfanar da kamfanin samar da allurar rigakafin AstraZeneca gaban kotu, kan bukatar tilasta masa samar wa da yankin alluran guda miliyan 90 kafin nan da watan Yuli mai zuwa.

Allurar rigakafin AstraZeneca
Allurar rigakafin AstraZeneca Alain JOCARD AFP/Archivos
Talla

A cewar kungiyar tarayyar Turan, tana bukatar kotu ta tilastawa kamfanin na AstraZeneca samar wa da yankin allurai guda miliyan 90, Kari a kan guda miliyan 30 da ya riga ya samar musu a farkon shekarar nan.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kamfanin ya gaza cika alkawarin da ya dauka na samar wa da yankin miliyoyin allurai ta cikin yarjejeniyar da suka kulla.

EU  din ta shigar da kararraki biyu kan kamfanin, na farko a wata kotu da ke Belgium bisa zarginsa da kin samar da alluran a kan lokaci, sai kuma yanzu da ta kara shirin gurfanar da ita kan rashin bata cikakkun alluran.

A cewar EU abin da Kamfanin na AstraZeneca ya yi zamba ne cikin aminci da kuma karya alkawarin da suka dauka na samar wa da yankin allurai miliyan 300.

Kamfanin AstraZeneca ya mayar da maratani, inda ya ce yana iya kokarinsa na cin karfin aikin samar da rigakafin a lokacin da ake bukata, duk da cewa yana karo da matsaloli a aikin samar da alluran rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.