Isa ga babban shafi
Faransa - Coronavirus

An sake bude gidajen abinci da shaye-shaye a Faransa

Gwamnatin Faransa ta bada umarnin sake bude gidajen abinci da na shaye-shaye gami da na kalankuwar al’adamu da kuma Sinima a yau Laraba, abinda ya kawo karshen tsawon lokacin da suka kasance a garkame domin dakile yaduwar annobar Korona.

Wasu Faransawa da suka fara morar karin kumallo a gidajen cin abinci ranar Laraba 19 ga watan Mayu 2021, bayan dage dokokin rufe gidajen saboda annobar korona
Wasu Faransawa da suka fara morar karin kumallo a gidajen cin abinci ranar Laraba 19 ga watan Mayu 2021, bayan dage dokokin rufe gidajen saboda annobar korona AP - Jean-Francois Badias
Talla

Karo na farko kenan da aka bude gidajen adana kayan tarihi, Sinima gidajen abinci da kuma na shaye-shaye a Faransa, tun bayan rufe da gwamnati tayi a watan Oktoban shekarar bara, sakamakon tsanantar annobar Korona da ta sake barkewa zango na biyu a sassan kasar.

A karkashin matakin soma sassauta dokokin takaita walwalar jama’ar da gwamnatin faransa ta soma aiwatarwa, wuraren taruwar jama’ar da suka hada da Sinima, gidajen adana kayan tarihi da kuma na abinci za su takaita yawan mutanen da za su dauka ne zuwa kashi 50 cikin 100, zalika taruka a harabobinsu zai kasance na adadin takaitattun mutane.

Dokar hana fitar dare kuwa ta karfe 7 zuwa asuba da ke aiki a fadin kasar ta Faransa domin dakile annobar Korona a yanzu ta koma daga karfe 9 na dare zuwa Safiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.