Isa ga babban shafi
Faransa - Sahel

Dakarun Tukuba sun shiga cikin jerin sojojin Faransa da suka yi faretin Bastille

Dakarun Soji na musamman daga kasashen Turai da zasu taka rawa a cikin sabuwar rundunar yaki da 'yan ta’adda a Yankin Sahel da aka yiwa suna Takuba zasu shiga cikin jerin sojojin da za suyi farati yau lokacin bikin ranar ‘Yancin Faransa da ake kira Bastille Day.

Sojojin Faransa maza da mata sama da 4400 a sun hallara faretin ranar Basille a dandalin Champs-Élysées, 14 ga watan Yuli 2021.
Sojojin Faransa maza da mata sama da 4400 a sun hallara faretin ranar Basille a dandalin Champs-Élysées, 14 ga watan Yuli 2021. AP - Lewis Joly
Talla

Akalla sojoji 80 daga Faransa da kasashen Turai zasu jagorancin faretin, a wani yunkuri na aikewa da sakon diflomasiya daga Paris.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirin janye dakarun kasar a watan jiya, inda yake fatar ganin sauran kasashen Turai sun bada gudumawar sojojin da zasu cigaba da yaki da yan ta’adda.

Shugaba Emmanuel Macron da Franministan Jean Castex yayin bukin ranar Bastille na 14 ga watan Yuli a Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron da Franministan Jean Castex yayin bukin ranar Bastille na 14 ga watan Yuli a Faransa. © AP/Ludovic Marin

Faransa na bukatar sabuwar rundunar ta Takuba ta kunshi sojoji 600, rabi daga kasar ta, domin maye gurbin sojojin ta 5,100 dake aiki yanzu a karkashin rundunar Barkhane.

Sojojin Faransa dake kula da karnuka da suka hallara faretin ranar Basille a dandalin Champs-Élysées, 14 ga watan Yuli 2021.
Sojojin Faransa dake kula da karnuka da suka hallara faretin ranar Basille a dandalin Champs-Élysées, 14 ga watan Yuli 2021. AP - Lewis Joly

A karon farko faretin zai koma fadar shugaban kasa, sakamakon yadda annobar korona ta hana bara, sai dai a wannan karon mutane 10,000 zasu kalli bikin, sabanin 25,000 da aka saba gani.

Masana yanayi sun yi has ashen cerwar ruwan sama na iya dakushe bikin nay au.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.