Isa ga babban shafi
Faransa - Afghanistan

Faransa na tattaunawa da Taliban kan kwashe mutane daga Afghanistan

Shugaba Emmanuel Macron ya ce Faransa na cikin tattaunawa da kungiyar Taliban a game da yanayin jinkai  a Afghanistan da kuma yiwuwar kwashe karin mutanen da ke cikin hadari, biyo bayan karbe mulki da kungiyar ta yi a ranar 15 ga watan Agusta.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS - POOL
Talla

Macron wanda ya ce Faransa ta kwashe mutane dubu 2 da 834 tun daga ranarr 17 ga watan Agusta, ya ce tare da Qatar suka tsara aikin kwashe mutanen.

Qatar na da kyakkyawar dangantaka da Taliban tun bayan da ta karbi bakunci tattauna batun janye sojin Amurka daga Afghanistan.

Wannan bayanan na Macron na zuwa ne a taron manema labarai a babban birnin Bagadaza na Iraqi, inda ya ke halartar taro a kan tsaron Gabas ta Tsakiya da zummar kawo karshen zaman tankiya a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.