Isa ga babban shafi
Faransa - Turai

Faransa ta bukaci gina sabuwar Turai mai cin gashin kai a siyasance

Ministan Tattalin Arzikin Faransa Bruno Le Maire ya roki kasashen yammacin Turai da su gina sabuwar nahiyar mai karfi gami da 'yancin siyasa da kuma ikon mallakar fasaha ta kansu, domin gogayya da Amurka da China.

Ministan Tattalin Arzikin Faransa Bruno Le Maire
Ministan Tattalin Arzikin Faransa Bruno Le Maire REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Le Maire ya bayyana haka ne yayin halartar Taron da ake yiwa lakabi da Ambrosetti kan makomar tattalin arzikin nahiyar Turai, wanda ke gudana yanzu haka a Italiya.

Yayin da Faransa ke shirin karbar ragamar shugabancin majalisar ministocin Turai a watan Janairu ministan kudin kasar Bruno Le Maire ce ya zama dole nahiyar Turai ta zama mai cin gashin kanta a fannin. siyasa kafin cimma irin burin a fannin fasaha da kere-kere. Dan haka ya zama dole kasashen Turai su karkata akalar manyan kamfanonin fasaha zuwa gare su, domin bunkasa fannonin su na kimiya da fasaha da kuma lafiya.

Yanzu haka dai Faransa na cimma yarjejeniya tsakanin kasashen Turai kan mafi karancin harajin da za su rika karba da manyan kamfanonin duniya.

Sai dai Ireland, Hungary da Estonia ba sa son shiga yarjejeniyar da kasashen G20 suka cimma a watan Yuli, wanda ta tanadi karbar harajin akalla 15% daga manyan kamfanonin duniya kan ribar suke samu a shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.