Isa ga babban shafi
Iceland

Turai: Iceland ta zama kasa ta farko mai mata fiye da maza a majalisar dokoki

Iceland ta zama kasa ta farko a Turai da ke da yawan mata fiye da maza a zauren majalisar dokoki, kwana guda bayan babban zaben ranar Asabar da ya sanya makomar gamayyar kawancen masu tsattsauran ra’ayi da masu sassaucin ra’ayin cikin shakku duk da cewa sun samu gagarumin rinjaye.

Firaministan kasar Iceland Katrin Jakobsdottir.
Firaministan kasar Iceland Katrin Jakobsdottir. © REUTERS - NTB SCANPI
Talla

Mata 33 ne dai suka lashe kujeru 33 daga cikin 63 na majalisar kasar ta Iceland, kwatankwacin kashi 52 cikin 100.

Babu wata kasar Turai da ta sami mata sama da kashi 50 cikin 100 na 'yan majalisa, inda Sweden ke kusa da kashi 47 cikin 100, a cewar wani sakamakon bincike da Bankin Duniya ya tattara.

Zuwa yanzu dai kassahe 5 ne kacal a Duniya ke da yawan mata ‘yan majalisu da suka kai fi rabin majalisun dokokinsu, ko kuma suka yi kan-kan-kan da maza ko kuma kusan rabin yawan wakilan zauren, inda Rwanda ke kan gaba da kashi 61 sai Cuba da kashi 53 kana Nicaragua da kashi 51 sannan Mexico da da Hadaddiyar Daular Larabawa dukkaninsu da kashi 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.