Isa ga babban shafi
Faransa-Girka

Faransa za ta samar da jiragen yaki ga Girka

Gwamnatin Girka ta kulla wata yarjejeniya da Faransa don samar mata da jiragen yaki guda uku, abin da ake ganin yana cikin shirye-shiryen da Girka ke yi na tunkarar Turkiyya kan rikicin gabar teku da ke tsakaninsu.

Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis da shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis da shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Ludovic Marin POOL/AFP
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis ta cikin wata sanawar hadin gwiwa da suka fitar, sun ce yarjejeniyar cinikin jiragen yakin da suka kulla za ta amfani kasashen tarayyar Turai da ma kungiyar NATO, ta hanyar tabbatar da tsaron yankin Mediterranean, kudancin Amurka, Gabas ta tsakiya da kuma kasashen Balkans.

Turkiyya wadda tuni da ma ba ta da kyakyawar alaka da kungiyarta NATO, makwafciya ce ga Girkan, na shan suka kan yi wa tsaron yankin da na kasashe makotanta barazana.

A cewar Firaministan Girka Kyriakos, mambobin majalisar tarayyar kasar su 300 sun amince da kulla yarjejeniyar cinikayyar jiragen yakin da Faransa, haka kuma shirin ya sami goyon bayan jam’iyyun siyasa biyar na kasar.

A cewarsa, Girka ta lura da irin take-taken Turkiyya na haddasa rikici tsakanin kasashen da ke makwaftaka da ita tun bayan da ta mamaye Cyprus, a don haka ya zama dole ta daura dammarar kare kanta ta hanyar tanadar kayan yaki don jiran ko ta kwana.

Wannan ciniki dai, ana ganin zai dan rage wa Faransa raradin da take ji, kan batun kwace cinikayyar jiragen yakin karkashin teku da ta kulla da Ausrtalia da Amurka ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.