Isa ga babban shafi
Turai-Coronavirus

Hukumar EU na nazari kan sabon maganin Covid-19

Hukumar da ke sa ido kan magunguna ta kungiyar tarayyar ta ce, ta fara yin nazarin maganin Covid da za a rika sha wanda kamfanin harhada magunguna na Amurka Merck ya samar da nufin saukaka hanyoyin yakar cutar.

Nau'in maganin Merck
Nau'in maganin Merck Handout Merck & Co,Inc./AFP/File
Talla

Wani kwamitin kungiyar da ke lura da al’amuran sarrafa magungunan bil’adama ya fara yin bita kan rigakafin, wanda Merck Sharp & Dohme ya samar tare da hadin gwiwar Ridgeback Biotherapeutics don maganin Covid-19, in ji sanarwar Hukumar Magunguna ta Turai.

Sakamakon farko ya nuna cewa maganin na iya rage karfin cutar a cikin jiki.

An dai gudanar da gwaji kan wasu marasa lafiya tsawon kwanaki, inda aka gano samun sassaucin hadarin ta ga jikin dan adama.

Idan har an amince da maganin, kwararrun sun ce zai taimaka kwarai wajen rage tasirin cutar, wanda kuma zai rage mace-macen da ake fama da shi da kashi 100.

Da zarar an tattara isassun bayanai, wani kamfani zai iya gabatar da bukatarsa don samun maganin da Hukumar Tarayyar Turai ta amince da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.