EU ta amince da wasu magungunan Korona
Hukumar Kula da Magunguna ta Tarayyar Turai ta amince da wasu magungunan kare da kuma inganta garkuwar jikin dan Adam daga kamuwa da Cutar Korona, karon farko kenan da ta amince da irin wadannan magunguna da nufin dakile ci gaba da yaduwar cutar.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta amince da maganin da aka yi wa lakabi da Ronapreve wanda hadin gwiwa ne tsakanin wasu kamfanonin samar da magunguna na kasashen Switzerland da Amurka da kuma Korea ta kudu.
Wannan dai na a matsayin wani mataki a yakin da duniya ke yi da ci gaba da yaduwar cutar ta Korona.
Wadannan kamfanoni su ne na farko da suka fara samun irin wannan sahalewa daga Hukumar Kula da Magunguna ta Tarayyar Turai a matsayin guda daga cikin makaman yaki da Korona.
Da take jawabi, Kwamishiniyar Lafiya ta Tarayyar Turai, Stella Kyrakides ta ce amincewa magungunan wani babban mataki ne ga yaki da cutar da kuma nahiyar Turai baki daya, kuma tuni EU din ta bukaci kamfanonin da su samar da magunguna guda miliyan 55 don fara gwaji a cewarta.
Sai dai ta ce har yanzu ba ta gama tantancewa idan mutane masu yawancin shekaru za su iya amfani da magungunan ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu