Belarus ta soma kwashe yan cin rani dake kan iyakar kasar
Hukumomin kasar Belarus sun kwashe ‘yan cin ranin da suka yi cincirindo a kan iyakar kasar da Foland tun farkon makon jiya, a wani yunkuri na kasar wajen kawo karshen matsalar ‘yan cin ranin da ta ki ci taki cinyewa.
Wallafawa ranar:
Hukumomin Belarus na cewa tuni aka kwashe ‘yan cin rani dubu 2 daga kan iyakar kasar da Foland tare da kai su sansani na musamman da aka samar musu.
Batun yunkurin kwarar ‘yan ciranin dai ya tayar da cece-kuce a tsakanin hukummin tarayyar Turai da Alexandra Lukashenko na Belarus, sakamakon zargin sa da goyawa ‘yan ciranin baya don shiga Turai da gangan.
Kwashe ‘yan ci ranin da mafi yawancin su suke daga Gabas ta tsakiya na bufin sassautowa daga kujerar nakin da Alexandra Lukashenko ya hau tun da fari, wajen sanya baki ko daukar wani mataki da ya dace game da al’amarin ‘yan ci ranin.
Jaridar Belta ta kasar ta wallafa Hotunan ‘yan Ciranin kwance kan Katifu lullube da barguna tare da rubuta cewa a karon Farko bayan shafe makkoni cikin tsananin sanyi, wannan shine daren su na Farko cikin dakuna.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa zasu dauki matakin Kula da ‘yan ci ranin har zuwa lokacin da abubuwa zasu dai-daita musamman tsakanin ta da kasashen da ‘yan ciranin ke da nufin shiga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu