'Yan sandan Finland sun kame mutane 5 dake shirin kai hare-haren ta'addanci
'Yan sanda a kasar Finland sun sanar da kame wasu mutane biyar masu tsatsauran ra'ayi da ake zargi da shirya kai hare-haren ta'addanci ta hanyar amfani da bama bamai da kuma bindigogi.
Wallafawa ranar:
Jami'an tsaron sun shaidawa wani taron manema labarai cewar, mutanen biyar dukkaninsu daga Kankaanpaa dake kudu maso yammacin kasar ta Finland ‘yan shekaru kusan 25 ne, wadanda aka kama su da safiyar ranar Talata bayan shafe shekaru biyu ana sa ido akansu.
Mai Magana da yawon ‘yan sandan na Finland Sufeto Toni Sjoblom ya ce sun gano adadi mai yawa na bindigogi, alburusai da ababen fashewa yayin binciken da ya gudana gidan masu tattsauran ra’ayin cikin Disamban shekarar 2019 lokacin da aka taba kama su bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Bincike dai ya nuna cewar da alama mutanen na da akidar nuna wariyar launi da kuma kishin kasa dake da alaka da harbe-harben ‘yan bindigar da aka fuskanta a Amurka, inda masu tsattsauran ra’ayin ke da nufin haifar da rarrabuwar kawuna da rikicin kabilanci a cikin al'umma.
Jami'an tsaro dai sun ki bayyana wuraren da aka shirya kai harin, amma sun ce kamen ya zama karo na farko a Finland da ake zargin masu tsattsauran ra’ayi da shirin kai hare-haren ta’addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu