Isa ga babban shafi
Mata-Faransa

Birgitte Macron ta fusata game da zargin tantama kan Matantakarta

Jita-jita kan matantakar mai dakin shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya karade kafafen yada labaran kasar a yau laraba, wanda ke bayyana cewa Birgitte Macron tun farko an haife namiji gabanin sauya halittarta zuwa Mace, jita-jitar da ke zuwa watanni gabanin zaben kasar da Macron ke neman wa’adi na biyu.

Shugaba Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte Macron.
Shugaba Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte Macron. AFP / Mandel Ngan
Talla

Lauyan Birgitte, Jean Ennouchi ya shaidawa manema labarai cewa tuni mai dakin shugaban ta fara shirye-shiryen shigar da kara kan batun wanda ta bayyana a matsayin taba kimarta.

Bayanai sun ce Birgette wadda ko a bara ta fuskan

Tun farko jita-jitar ta fara tsananta ne a kafafen sada zumunta kan zargin cewa Birgitte mai shekaru 68 ta sauya halittarta ne zuwa mace gomman shekaru da suka gabata.

Jita-jitar sauyin halitta ba sabon abu ba ne tsakanin fitattun mutane musamman ‘yan siyasa amma kuma bai taba faruwa a Faransa in banda yanzu akan Birgette ba.

Kafin yanzu dai mai dakin tsohon shugaban Amurka Michelle Obama ta fuskanci makamancin wannan zargi haka zalika mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris kana Firaministar New Zealand Jacinda Arden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.