Isa ga babban shafi
Faransa-Mata

Mata za su ci moriyar magunguna hana daukar ciki kyauta a Faransa

Faransa ta gabatar da wani tsarin fadada shirin tazarar iyali da ya sahalewa mata ‘yan kasa da shekaru 25 karbar kwayoyin hana daukar ciki kyauta kuma cikin sauki a wani yunkuri na dakile kananan yaran daga daukar ciki baya ga hana su karaya daga shan magungunan saboda tsadarsu.

Sashen karbar magunguna hana daukar ciki a birnin Paris na Faransa.
Sashen karbar magunguna hana daukar ciki a birnin Paris na Faransa. Sarah Elzas/RFI
Talla

Shirin wanda zai shafi yaran mata miliyan 3 tun kafin sabon tsarin kasar na bayar da kawayoyin hana daukar cikin kyauta ne amma ga mata ‘yan kasa da shekaru 18 sai dai sabon tsarin wanda zai fara aiki daga yau 1 ga watan Janairu ya sahalewa hatta mata ‘yan shekaru 25 karbar kwayoyin kyauta.

Kwayoyin hana daukar ciki ga kananan yara dai kyauta ne a kasashen Turai irinsu Faransar da Belgium  da Jamus da Netherlands da Norway yayinda Birtaniya ke bayar da shi hatta ga manya ba tare da kudu ba.

A watan Satumba ne Faransa ta sanar da shirin kara yawan wadanda za su ci gajiyar kwayoyin kyauta zuwa har ‘yan shekaru 25 saboda yadda tsadarsu ke hana matan siya kuma suke karewa da daukar cikin da basu shiryawa ba.

A cewar ma’aikatar tattalin arziki ta Faransar, ta bakin kakinta Louise Delavier matakin kara masu cin gajiyar kyautar kwayoyin hana daukar cikin na da nasaba da yadda alkaluma suka nuna musu wahalhalun da mata ke haduwa da su ta fuskar tattalin arziki idan suka haifi ‘ya’yan da basu shirya musu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.