Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta laftawa kamfanin Google tarar Yuro miliyan 150

Hukumar da ke sa ido kan kare bayanan sirri na masu shiga shafukan Intanet a Faransa, ta ci tarar kamfanin Google Yuro miliyan 150, yayin da kuma ta laftawa Facebook tarar Yuro miliyan 60.

Faransa na tuhumar Facebook da Google kan laifin rashin mutunta dokar 'yancin masu amfani da shafukansu na Intanet.
Faransa na tuhumar Facebook da Google kan laifin rashin mutunta dokar 'yancin masu amfani da shafukansu na Intanet. DENIS CHARLET AFP/File
Talla

Matakin ya biyo bayan samun kamfanonin da laifin kin saukakawa masu amfani da Intanet na kasar wajen yin watsi da fasahar Cookies da ke bibiyar bayanan wayoyi ko kamfutocin da aka yi amfani da su wajen shiga shafukansu.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Hukumar Kula da Fasahar Watsa Labarai da kuma ‘yanci ta Faransar, ta ce bincikenta ya gano cewa Facebook, Google da kuma dandalin bidiyo na Youtube suna tilastawa masu shiga shafukansu bin matakai ko zabi da dama, kafin basu damar kin karbar fasahar tattara wasu daga cikin bayanan na’urorinsu wato 'Cookies' a turance, matakin da ya keta 'yancin masu amfani da Intanet.

Tun cikin shekarar 2018 ne dai kungiyar tarayyar Turai EU ta kafa dokar tilastawa kamfanonin sadarwa saukakawa masu shiga shafukansu zabin karba ko watsi da Cookies.

A halin yanzu kuma, hukumar ta sa ido kan kare bayanan sirrin masu amfani da Intanet a Faransar ta baiwa Google da Facebook watanni uku don yin biyayya ga umarninta don saukaka tsarin kin karbar coolies, ko kuma su fuskanci karin hukunci na alfta musu tarar Yuro 100,000 a kowace rana.

A watan Yulin shekarar 2021 Hukumar da ke sa ido kan daidaita gasa tsakanin kafanonin fasahar sadarwa a Faransa ta ci tarar Google Yuro miliyan 500 saboda kin biyan diyya yadda ya kamata ga kamfanonin watsa labaran da kamfanin na Google ya rika amfani da bayanansu a shafukansu na ba da bayanan bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.