Isa ga babban shafi
Kazakhstan

Fiye da mutane 220 ne suka mutu a rikicin Kazakhstan - Gwamnati

Gwamnatin Kazakhstan ta ce mutane 225 suka mutu a rikicin da ya barke a kasar, wanda ya fara daga zanga-zangar lumana a farkon watan Janairu, kan tsadar rayuwa.

Yadda wani yankin kasar Kazakhstan ya kasance, bayan rikidewar zanga-zanga kan tsadar rayuwa zuwa tarzoma.
Yadda wani yankin kasar Kazakhstan ya kasance, bayan rikidewar zanga-zanga kan tsadar rayuwa zuwa tarzoma. AP - Vladimir Tretyakov
Talla

Sabbin alkaluman sun bayyana cewar 19 daga cikin wadanda suka mutu a rikicin jami’an tsaro ne, sai kuma fararen hula da ‘yan bindigar da suka yi wa zanga-zangar shigar bazata.

Bayan rikidewar zanga-zangar da aka fara zuwa tarzoma da kuma arrangama tsakanin wani gungun mutane masu makamai da jami’an tsaro ne, shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya ayyana dokar ta-baci tare da neman agaji daga wata kungiyar gamayyar sojojin kasa da kasa da ke karkashin jagorancin Rasha.

Da fari dai mutane kusan 50 kawai gwamnatin Kazakstan ta ba da sanarwar sun mutu a rikicin da ya barke, wadanda ta ce 18 jami'an tsaro ne sai kuma ‘yan bindiga 26.

Sai dai a halin da ake ciki, sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta tabbatar, sun nuna cewar baya ga mutane 225 da suka halaka, wasu fiye da dubu 2 da 600 ne suka jikkata, 67 daga cikinsu kuma na cikin mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.